Man U na shirin sayo Zaha, Man City za ta kashe makudan kudi

Wilfried Zaha Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wilfried Zaha

Manchester United na shirin fitar da kudi fan miliyan 70 domin sake sayo dan wasan Crystal Palace Wilfried Zaha, mai shekara 26, wanda ya kasance tare da su a tsakanin 2013 da 2015. (Sun)

Liverpool na shirin tattauna wa da dan wasan Scotland Ryan Fraser, mai shekara 25, daga Bournemouth a watan Janairu. (Talksport)

Tottenham ta shirya tayin tsohon dan wasan Lyon mai shekara 25, Memphis Depay, a kan kudi fan miliyan 50 wanda ya taka leda a Manchester United tsakanin shekarar 2015 zuwa 2017. (Mirror)

Tsohon dan wasan Liverpool Xabi Alonso, mai shekara 37, da kocin Tottenham Mauricio Pochettino, mai shekara 47, na cikin jerin 'yan takarar kujararar tsohon kocin Bayern Munich da aka kora Novac Kovic. (Star)

Rahotanni na cewa Manchester City na shirin kashe kudi kusan fam miliyan 100 a kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu, bayan da ta gaza kai bantanta a wasan da suka fafata da Liverpool a gasar Premier. (Mirror)

Rahotanni na cewa Manchester United ba ta da niyyar sayen tsohon dan wasan gabanta,Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, a watan Janairu. yayin da kwantiraginsa a LA Galaxy ya kusa karewa. (Sky Sports)

Golan Arsenal Gernd Leno, mai shekaru 27, da alama dai zai maye gurbin Manuel Neuer mai shekara 33 a Bayern Munich yayin da kungiyar ta kyalla ido a kan sa (Sun)

Borussia Dortmund har yanzu dai tana zawarcin dan wasan gaba na Everton Anthony Gordon, mai shekara 18, duk da an ki tayin dan wasan dan kasar Ingila. (Football Insider)

Za a bai wa kocin Arsenal Unai Emery dama a wasanni shida masu zuwa da kungiyar za ta yi domin tabbatar da cewa zai iya ci gaba da jagorantar kungiyar. (Standard)

Tsohon kocin Spain Luis Enrique, wanda ake ganin zai iya maye gurbin Emery a Arsenal, ba ya tunanin komawa kungiyar a yanzu. (ESPN)

Dan wasan Newcastle Matty Longstaff, mai shekara 19, zai rattaba hannu kan wata sabuwar kwantaragi a 'yan makwanni masu zuwa sai dai an shaida wa dan uwansa mai shekaru 22, Sean ya nuna bajinta daga nan zuwa watanni 12 don samun sabuwar yarjejeniya. (Telegraph)

Dan wasan gaban Spain Ayoze Perez, mai shekara 26, ya bayyana cewa ya janye komawarsa Valencia daga Newcastle a lokacin bazara. (Mail)

Tottenham, Chelsea, Watford da Norwich sun shirya tayin dan wasan Metz Habib Diallo a watan Janairu. Dan wasan dan kasar Senegal mai shekara 24 ya zira kwallaye takwas a wasanni 13 da ya buga zuwa yanzu. (Teamtalk)

West Ham na duba yiyuwar sayen sabon mai tsaron raga a watan Janairu, bayan da kungiyar ta gaza tantance yanayin Roberto. Dan wasan dan kasar Spain, mai shekara 33 kwallaye 13 ya tare wa kungiyar a wasanni shida na Premier tun bayan da ya maye gurbin Lukasz Fabianski da ya tafi hutun jinya. (The Athletic - subscription required)

Kocin Hammers Manuel Pellegrini na kokarin samo mafitar da zai kare kansa bayan nasarar da suka samu a hannun Burnley. (Sun)