Kyaftin din Newcastle ba zai sake buga wasa ba sai a 2020

Kyaftin din Newcastle Jamaal Lascelles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kyaftin din Newcastle Jamaal Lascelles

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta ce kyaftin dinta, Jamaal Lascelles zai tafi hutun jinya har zuwa watan Janairun badi.

Dan kwallon mai shekaru 26, an maye gurbinsa ne bayan mintina 20 a wasan da kungiyarsa ta samu galaba a kan Bournemouth da 2-1 a gasar Premier ranar Asabar.

Lascelles, wanda aka fitar da shi daga filin wasan a kan makara, ya ja gaba don ganin kungiyarsa ta tabuka rawar gani a wannan karon.

Newcastle ce a matsayi na 13 a saman tebur bayan nasarar da suka samu karon farko a kakar wasa ta bana.

Da alama dai kungiyar za ta kara kaimi a kakar bana, kasancewar akwai wasanni masu zafi a gaban ta a Premier.

Labarai masu alaka