Man City ta samu fiye da fam miliyan 500 - Guardiola

Manchester City ta lashe Kofin Premier, FA, Kofin League a bara Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Manchester City ta lashe Kofin Premier, FA, Kofin League a bara

Manchester City ta fitar da rahoton kudaden shigar da ta samu daga shekarar 2018 zuwa 2019 da suka tasamma sama da fam miliyan 535.

Wannan ne shekara ta 11 da Man City ke samun karuwar kudin shiga yayin da ta ke gab da kamo Manchester United, wato kulob mafi karfin arziki a Premier Ingila.

An yi hasashen cewa alkaluman za su karu daga nan zuwa shekara mai kamawa, idan har Man City din ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi.

Manchester United ta ce samun kudin shigarta zai fada tsakanin fan miliyan 560 zuwa 580 a wannan shekara saboda gazawarsu ta zuwa gasar Zakarun Turai.

Adadin dai ya kunshi yadda 'yan wasan City da suka kunshi maza da mata suka samu nasarar lashe kofuna shida, gami da kyakkyawar lambar yabo ga kocin kungiyar Pep Guardiola.

Shugaban kungiyar, Khaldoon al-Mubarak ya ce "Wannan sakamakon ba kawai ya shafi lokacin kakar wasa ba, ya shafi tsawon shekaru 10 da kungiyar ta dauka tana aiki ba ji ba gani."

Tana wani matakin na cigaba wanda ya ba mu damar yin tsari a cikin jerin shekaru masu yawa."

City ta samu ribar fam miliyan 10 da kuma ribanya albashi da kaso 59.