Makomar Rodriguez, Sancho, Mandzukic, Can, Mbappe da Willian

Mbappe Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal za ta ware fam miliyan £35 domin karbo dan wasan tsakiya na Real Madrid dan kasar Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, wanda aka fi sa ran zai fi son ya koma Inter Milan ko Paris St-Germain. (Eldesmarque - in Spanish)

Wasu rahotanni sun ce Rodriguez yana son ci gaba da taka leda a Real Madrid inda yake son tabbatar wa Zinedine Zidane cewa yana kan ganiyarsa. (Marca)

Dan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 20, zai koma Real Madrid. (Le Parisien - in French)

Dan wasan Real Madrid na Uruguay Fede Valverde, mai shekara 21, ya tsawaita kwangilar shi har zuwa 2025. (Marca)

Flamengo ta fara tattaunawa da Atletico Madrid kan tsohon dan wasanChelsea Diego Costa, mai shekara 31. (Goal.com)

Chelsea za ta sake tattaunawa da dan wasanta na Brazil Willian, mai shekara 31, kan makomarsa. (Telegraph)

Borussia Dortmund ta ce a shirye ta ke ta saurari bukatar dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19, idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa a Janairu. (The Independent)

Sancho wanda ya fara kuriciyarsa a Manchester City zai iya karawa gaban Liverpoola cewar tsohon dan wasan kungiyar Jamie Carragher. (Daily Star)

Manchester United ta jingine sha'war karbo dan wasan Juventus dan kasar Croatia Mario Mandzukic, mai shekara 33. (The Athletic, via Inside Futbol)

Borussia Dortmund na son karbo Mandzukic da kum dan Emre Can na Juventus mai shekara 25. (Sun)

Milan na son karbo dan wasan Juventus na kasar Turkiya Merih Demiral, mai shekara 21 wanda Manchester City daArsenalke hamayya akan sa. (Calciomercato)

Labarai masu alaka