Premier League: Leicester City ta ci gaba da jan zarenta

Tawagar Leicester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu Leicester ba ta yi rashin nasara ba a gidanta a Premier bana

Leicester City ta ci gaba da jan zarenta a Premier sakamakon lallasa Everton 2-1 da ta yi a wasan mako na 14.

Har yanzu kungiyar ba ta yi rashin nasara a gidanta ba a Premier, sai dai a duka wasannin kakar bana da ta buga wannan na cikin wasannin da ta sha wuya kafin ta samu nasarar samun makinta.

Tun a minti na 23 ne Richarlison jefa wa Liecester kwallo daya a raga, duk da cewa ita ce take rike da ragamar wasan.

Bayan canjin da Liecester ta yi a minti na 62 - ta cire Ayoze Perez, Kelechi Iheanacho ya shigo - shi ne ya ba ta damar farke kwallonta a minti na 68, inda Jamie Vardy ya farke kuma wasa ya zama 1-1.

Hakan ya sa Vardy ya zama dan wasan da ya fi kowanne zira kwallo a raga a Premier - ya ci 13.

An yi karin minti shida bayan cikar minti 90, a lokacin ne Kelechi Iheanacho ya jefa kwallo ta biyu a ragar Everton, wadda ita ce kwallonsa ta farko cikin wasan Premier 25 da ya buga kuma ita ce ta farko a Premier bana.

Sai da aka kai ruwa rana kafin na'iurar VAR ta tabbatar da kwallon da Iheanacho ya ci, inda aka yi njiran minti daya da dakika takwas. Kwallon dai ta zo da rudani, inda mataimakin alkalin wasa ya ce an yi satar gida.

Leicester ce ke biye wa Liverpool baya a saman teburin Premier. Nasarar ta ba ta damara hada maki 32 - maki takwas a kasan Livedrpool din.

Watford ce kungiyar gaba da Leicester za ta buga wasa da ita, kafin daga bisani ta je Manchester City sannan kuma ta karbi bakuncin Liverpool duka a watan Disamba.

Labarai masu alaka