Ballon d'Or: Messi, Ronaldo ko Van Dijk?

Luka Modric Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bara Luca Modric ne ya lashe kyautar

A ranar Litinin din nan ne za a sanar da gwarzon dan kwallon duniya na Ballon d'Or.

Dan wasan bayan Liverpool Virgil van Dijk na daya daga cikin wadanda suke kan gaba a sunayen 'yan takarar da aka fitar.

Idan dan wasan ya samu wannan kyauta, zai kasance dan wasan baya na farko kenan tun bayan wanda ya lashe gasar shekaru 13 da suka gabata.

'Yan wasan Premier ne dai suka mamaye gasar, yayin da sunaye 15 suka fito daga cikin mutum 30. Amma wanene zai lashe gasar?

A bara Luka Modric ne kadai ya sha gaban Lionel Messi da Cristiano Ronaldo tun bayan shekara 11 da suka mamaye gasar.

Ronaldo da Messi kowannensu ya lashe gasar har sau biyar a baya.

Messi ne ya lashe gwarzon FIFA na bana, yayin da Van Dijk ya kasance gwarzon EUFA na bana.

Ronaldo ya taimaka wa kungiyarsa lashe gasar Serie A, yayin da ya taimaka wa kasarsa samun gurbi a gasar Euro 2020.

Labarai masu alaka