An bukaci hukumar FA ta binciki ihun da aka wa Chelsea

West Ham ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar Premier ranar Asabar Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption West Ham ta doke Chelsea da ci 1-0 a gasar Premier a ranar Asabar

Hukumar yaki da nuna wariya ta Birtaniya ta bukaci hukumar kwallon kafar kasar da ta yi binciken musabbabin ihun da magoya bayan West Ham United suka yi wa Chelsea.

Hukumar ta karbi korafe-korafen yadda aka yi wa magoya bayan Chelsea a Stamford Bridge ihu a ranar Asabar, a cewar hukumar.

Kungiyar magoya bayan Chelsea ta ce ta lura da yadda ake yi wa kungiyar ihun nuna wariya da ke da alaka da auren jinsi daga magoya bayan West Ham".

Sai dai kungiyar magoya bayan West Ham ta ce a bayyane yake korafin da hukumar yaki da nuna wariya ta shigar na da nasaba ne da nuna kyama ga auren jinsi.

A shafinta na Twiiter ta kara da cewa: "Idan ka yi amfani da alamun nuna kyama da auren jinsi, ba Chelsea kuka wa shagube ba, amma masu nuna goyon baya ga auren jinsi, ko da suna goyon bayan Chelsea ne ko kuma West Ham din.

"Mun wuce irin wannan danyen aikin, ya kamata mu bullo da wani abu na daban ga magoya baya, amma kar mu yi amfani da ihun nuna wariya wajen ci musu zarafi.

"Bai kamata kungiyarmu ta kasance mai kambama matsalar da ta shafi nuna wariya ba... Akwai wasu kulob-kulob din da suke da irin nasu tarin matsalolin.

"Kada muyi kokarin kasancewa a rukuninsu. Ya kamata mu gyara sunan kulob dinmu. Mu nuna goyon bayanmu ga magoya bayan West Ham, babu ruwanmu da launin fata, jinsi, da makamantansu."

"Mun fahimta cewa hukumar FA na sane da zargin kuma ana ci gaba da tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa."

Wani mai magana da yawun kungiyar Chelsea ya ce: "Kamar yadda muke sukar magoya bayan namu yayin da suka aikata laifin nuna wariya, muna sa ran sauran kungiyoyin za su tashi tsaye, su magance irin wannan matsalar.

A wata sanarwa da ta fitar, West Ham ta ce: "Ba za ta lamunci irin wannan dabi'ar da ta yi wa dokar hukumomin da abin ya shafa karan tsaye.