Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2019

A Hakkin mallakar hoto Ballond Or
Image caption Bana shi ne karo na shida ke nan da dan kwallon yake lashe kyautar

Dan wasan Argentina da kuma Barcelona, Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2019, wato Ballon d'Or ta 2019.

Messi ya ciyo wa kungiyarsa da kasarsa kwallaye 46 a shekarar 2019.

Dan kwallon ya doke 'yan wasa kamar su: Virgil van Dijk da Cristiano Ronaldo da Sadio Mane da Mo Salah da Kylian Mbappe da sauransu.

Bana ne karo na shida da dan wasan ya lashe kyautar.

Messi ya taba lashe kyautar a shekarar 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da kuma 2015.

Hakazalika 'yar wasan tawagar kwallon kafar Amurka, Megan Rapinoe ce ta lashe kyautar Ballon d'Or ta mata ta bana.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yar tana cikin tawagar Amurka wadda ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya na Mata a bana a Faransa

'Yar wasan mai taka leda a Reign FC, mai shekara 34, ta ci Kofin Duniya wanda aka yi a kasar Faransa a bana.

Golan kungiyar Liverpool Alisson Becker ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron gida ne a lokacin bikin karrama 'yan wasa wanda aka yi a birnin Paris a kasar Faransa ranar Litinin.

Labarai masu alaka