Ole Gunnar Solskjaer: Kocin Man Utd ba ya jin ko dar kan korar masu horaswa

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce sallamar da ake yi wa masu horaswa a baya-bayan nan ko a jikinsa, duk da cewa kungiyar ta fuskanci kakar bana da kafar hagu ne.

Tottenham ta kori Mauricio Pochettino a watan Nuwamba, kafin nan Arsenal ta sallami Unai Emery inda Watford ta raba gari da Quique Sanchez Flores.

United na kan matsayi na tara da maki 18 a saman teburin Premier, kakar wasa mafi muni da ta fara tun bayan shekaru 31 da suka gabata.

"Abinda na sanya a gaba shi ne aikina," in ji Solskjaer.

"Kuma abinda zan iya shi nake yi, musamman don ganin yadda za mu tunkari wasanninmu na gaba, sai dai muna ganin akwai sauran rina a gabanmu, amma muna kan tattaunawa da shugabannin kungiyar."

An danganta Pochettino da Man United kafin Solskjaer ya maye gurbin Jose Mourinho.

Da farko dai sun yi yarjejeniyar zai rike kocin kungiyar na wucin gadi, a watan Disambar 2018 inda ya ce "a shirye yake don karbar kowanne tayi da za a masa" saboda yana da niyyar "koma wa Turai".

Solskjaer ya kara da cewa "Lokaci ne ya yi. Babu dadi ka ga abokan aikinka suna rasa ayyukansu - misalin mutane ukun nan da suka rasa mukamansu.

"Wannan ba ya damuna ko kadan kan matakan da sauran kungiyoyi suke dauka.

"Ba ma jin dadin sakamakon da muke samu, amma kuma muna da yakinin samar da ci gaba."

Solskjaer zai kece raini da Mourinho - wanda ya maye gurbin Pochettino a Spurs - yayin da United za ta karbi bakuncin kungiyar da ke arewacin Landan a ranar Laraba.

Dan wasan tsakiya Paul Pogba bai sake takawa United din leda ba tun a watan Satumba, sakamakon jinyar raunin da yake yi, kuma Solskjaer ya ce dan wasan mai shekara 26 ba zai fito a wasan da Manchester United din za ta yi da Tottenham din ba.