Kocin Chelsea Frank Lampard na dakon hukuncin karar da suka daukaka

Kocin Chelsea Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Takunkumin da aka sanya wa Chelsea zai kare a watan Fabrairun 2020

Kocin Chelsea Frank Lampard yana fatan a sanar da shi matakin janye takunkumin da aka sanya wa kungiyar nan ba da jimawa ba.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ce ta haramta wa kungiyar sayen 'yan wasa, sakamakon karantsaye da ta yi wa dokarta na siyan wasu matasan 'yan wasa.

An dai shaida wa Chelsea kada ta yi gaggawar daukaka kara, ma'ana an hana ta damar kawo sabbin 'yan wasa a lokacin saye da siyarwar 'yan wasan.

Amma kotun sauraron kararraki kan al'amuran wasanni ta yi zama a watan jiya game da karar da Chelsea ta daukaka, kuma kungiyar na fatan samun nasara a karar nan da 'yan kwanaki.

Hukuncin da FIFA ta wallafa a shafinta ya nuna cewa kulob din ya saba wa doka 150 da ta hadar da daukar matasan 'yan wasan guda 69 a kakar wasanni da yawa ba bisa ka'ida ba.

Ko da aka tambaye shi yaushe sakamakon karara da suka daukaka zai fito, Lampard ya ce: "Nan ba da jimawa ba.

"Ban sake jin komai ba game da karar, don haka zan jira hukunci.

Kan shirin Chelsea na sayen 'yan wasa a watan Janairu kuwa, za mu jira hukuncin da kotu za ta yanke kafin mu dauki mataki na gaba.

Takunkumin da aka sanya wa Chelsea zai kare a watan Fabrairun 2020.

Labarai masu alaka