Everton: Richarlison ya tsawaita kwantaraginsa zuwa 2024

Richarlison ya koma Toffees daga Watford a watan Yulin 2018. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Richarlison ya koma Toffees daga Watford a watan Yulin 2018

Dan wasan gaban Everton Richarlison ya sanya hannun tsawaita kwantaraginsa zuwa kakar wasa ta shekarar 2024.

Richarlison ya koma Toffees daga Watford a watan Yulin 2018.

Dan wasan ya ciyowa kungiyar kwallaye 20 a wasanni 55 da ya yi mata.

Richarlison, mai shekara 22, ya fara bugawa kasarsa Brazil wasa watanni biyu bayan ya koma Everton, kuma yanzu haka ya buga mata wasanni 19.

"Ina da niyyar ci gaba da zama a nan. Wannan ce kungiyar da ta ba ni damar nuna bajintata a kwallon kafana," in ji Richarlison.

"A nan ne na samu damar shiga rukunin kasa ta Brazil kuma a nan ne na zira kwallaye da yawa a gasar Premier."

Tsawaita kwantiragin Richarlison ya zo ne kwana daya kafin wasan da Everton za ta fafata da masu jan ragamar Premier wato Liverpool a filin wasa na Anfield.

"Kulob din ya yarda da bajintata ni ma kuma na yarda da shi," a cewar dan wasan wanda ya zira kwallo a wasan da suka doke Leicester ranar Lahadi da ci 2-1.

"Magoya bayana suna nuna matukar kauna a gare ni kuma ina kokarin mayar da duk wannan kauna gwargwadon iko a filin wasa."

Labarai masu alaka