Fifa: Kudin wakilan 'yan wasa ya kai fan miliyan 500 a 2019

Cristiano Ronaldo tare da Jorge Mendes Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Cristiano Ronaldo tare da wakilinsa Jorge Mendes

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ce fiye da rabin fan biliyan daya aka kashe a kan wakilai da dillalan 'yan wasa a shekarar 2019 ciki har da batun cinikayyar 'yan wasa.

Rahoton da kwamitin gudanarwar kwallon kafa ta duniya ya fitar ya ce kudaden da aka kashe a matsayin tukwici sun kai kusan dala miliyan 653.9 kwatankwacin naira biliyan 236.

Hukumar ta ce an samu karuwar kudaden da ake kashewa da kusan kashi 20% idan aka kwatanta da shekarar 2018.

FIFA ta ce kashi 80% na adadin da aka kashe sun fito ne daga kungiyoyin kasashen Italiya, Ingila, Jamus, Portugal, Spain da Faransa.

Kungiyoyin Portugal sun kashe kudi sosai a kan tukwici fiye da yadda suke kashewa wurin hada-hadar 'yan wasa.

A farkon wannan shekarar, FIFA ta fitar da wasu jerin matakai domin takaita kudaden da ake kashewa wurin biyan dillalan 'yan wasan.

Hakan na nufin kada dillalan su karbi kudin da yawansa ya wuce kashi 10% na adadin kudin da aka sayi dan wasa.

Labarai masu alaka