Kwallon mata: Za a samu sauyi a Champions League ta mata

'Yar wasan Ingila Lucy Bronze ta taimakawa kungiyarta ta Lyon kare kambun kofin gasar. Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption 'Yar wasan Ingila Lucy Bronze ta taimaka wa kungiyarta Lyon cin kofin a karo na biyu

Hukumar shirya gasar Zakarun Turai ta Champions League za ta fitar da wani sauyi na matakin rukuni-rukuni a zagayen dab da na kusa da na karshe banagaren kwallon mata.

Sabon matakin zai fara aiki ne daga kakar wasa ta 2021-2022, kamar yadda Uefa ta tabbatar.

Daga lokacin kungiyoyi hudu ne za a kasa su cikin rukuni hudu a zagayen 'yan 16 na gasar, inda biyu daga kowanne rukuni za su je matakin kwata fayinal bayan sun fafata da juna a wasa gida da waje.

Wasu daga cikin kungiyoyin sai sun buga wasanni sama da haka kafin su kai wannan matakin - ya danganta da matakin da suka kare a gasar lig ta kasashensu.

Amma zakaru daga manyan gasanni na nahiyar Turai guda uku, ciki har da Ingila, za su wuce kai-tsaye zuwa matakin 'yan 16.

Tun daga shekarar 2009 ake yin wasa dai-dai a cikin rukuni daga farkon gasar, amma daga matakin 'yan 32 sai a rika yin wasa gida da waje.

Labarai masu alaka