Za a yi amfani da VAR a Euro 2020 da gasar Kofin Duniya

Anyi amfani da tsarin karon farko a gasar Premier ta bana. Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption An yi amfani da tsarin karon farko a gasar Premier ta bana

Za a yi amfani da na'urar VAR a wasan cike gurbi na gasar cin Kofin Turai a shekara mai zuwa, ana kuma shirin kaddamar da na'urar a wasannin share fagen shiga gasar cin Kofin Duniya ta 2022.

Na'urar taimaka wa alkalin wasan an gabatar da ita ne a gasar cin kofin nahiyoyi ta Confederation a 2017 kafin a yi amfani da ita a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a kasar Rasha.

Sai dai ba'a yi amfani da na'urar ba a wasannin share fagen shiga gasar Euro 2020.

Hukumar shirya Uefa mai kula da harkokin wasanni a nahiyar Turai, ta amince a gabatar da ita a wasan cike gurbi na Euro 2020 a watan Maris amma sai Fifa ta amince kafin a yi amfani da ita a wasannin shiga gasar cin Kofin Duniya.

Kasashen Scotland da Ireland ta Arewa da Jamhuriyar Ireland dukkansu suna cikin jerin kasashen da za su fafata a wasan cike gurbi na Euro 2020 wato play-off.

An yi amfani da tsarin a karon farko a gasar Premier ta bana.

Labarai masu alaka