Alderweireld ya sabunta kwangilarsa a Tottenham

Alderweireld

Asalin hoton, Getty Images

Dan kwallon baya na Tottenham, Toby Alderweireld ya sanya hannu a wata sabuwar yarjejeniya domin ci gaba da kasancewa tare da kungiyar har zuwa shekarar 2023.

Kwangilar dan kwallon na Belgium ya kamata ta kare ne a kakar wasan bana, kuma a yanzu babu sauran ce-ce-ku-ce kan makomarsa.

Alderweireld mai shekara 30, ya buga wa Spurs wasanni 179 tun lokacin da ya koma Ingila daga kungiyar Atletico Madrid a watan Yulin 2015.

"Babu inda zan kasance cikin murna kamar ci gaba da buga kwallo a nan," in ji Alderweireld.