Arteta ya zama kocin Arsenal

arteta

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Arsenal ta nada tsohon dan wasanta Mikel Arteta a matsayin sabon kocinta.

Dan shekara 37, ya lashe gasar kofin FA sau biyu tare da Gunners a shekara biyar da ya shafe yana murza leda tare da kungiyar.

Arteta dan kasar Spain ya maye gurbin Unai Emery wanda aka kora a watan Nuwamba.

Arteta ya yi aiki tare da Pep Guardiola a Manchester City tun bayan da ya yi ritaya a shekara ta 2016.

Arsenal ce ta 10 a kan teburin gasar Premier, inda kawo yanzu take da maki 22.

Ranar Asabar ake sa ran Arteta zai jagoranci Arsenal wasan farko, inda za su ziyarci Goodison Park a wasan mako na 18 tsakaninta da Everton.