Pogba na nan daram a United - Solskjaer

Pogba ya nuna cewa zuciyarsa ba ta United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pogba ya nuna cewa zuciyarsa ba ta United

Kocin Manchester United , Ole Gunnar Solskjaer ya ce 'ba za a sayar da' Paul Pogba a cikin watan Junairu ba.

Sannan kuma ya musanta cewa ya tattauna da dan wasan Red Bull Salzburg Erling Haaland a ranar Juma'a.

Pogba ya murmure daga raunin da ya ji amma kuma sai ya kamu da zazzabi abin da ya sa watakila ba zai buga wasansu da Watford a ranar Lahadi ba.

Solskjaer ya ce bai zai ce komai ba kan matashin dan kwallon Norway, Haaland wanda ake rade-radin zai koma United.

A kan batun Pogba, kocin ya ce "ba za mu sayar da shi ba a watan Junairu."