Algeria tana daga cikin masu yawan maki a 2019

Algeria

Asalin hoton, BBC Sport

Kasashe uku daga Afirka suna daga cikin guda 10 da suka samu yawan maki a jadawalin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa da ta sanar a 2019.

Algeria wadda ke rike da kofin nahiyar Afirka ta hada maki 135 a shekarar 2019, kasa da maki uku da wadda take ta daya Qatar, wadda ta hada maki a shekarar.

Duk da wannan kwazon da Algeria ta yi tana ta hudu a Afirka kuma ta 35 a duniya a jadawalin da Fifa ta bayyana na kasashen da ke kan gaba a tamaula.

Najeriya tana ta bakwai, ita kuwa Madagascar tana ta 10 a jerin wadan da suka samu maki da yawa a 2019.

Super Eagles wadda ta yi ta uku a gasar kofin nahiyar Afirka, tana ta uku a Afirka, sannan ta 31 a duniya.

Madagascar ita ce ta 21 a Afirka, sannan ta 91 a duniya, bayan da ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar.

Senegal ta ci gaba da zamanta a mataki na daya a Afirka ta 20 a duniya, sai Tunisia ta biyu a Afirka, kuma ta 27 a duniya.

Belgium ta ci gaba da zama ta daya a jerin kasashen da ke kan gaba a kwallon kafa a duniya, sai Faransa biye da ita sannan Brazil ta uku a duniya.

Jerin kasashen Afirka 10 da ke kan gaba wajen taka leda:

  • .Senegal
  • Tunisia
  • Nigeria
  • Algeria
  • Morocco
  • Ghana
  • Egypt
  • Cameroon
  • .Mali
  • Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo