Ramos ne kan gaba wajen buga El Clasico

Sergio Ramos

Asalin hoton, Real Madrid

A ranar Laraba ne aka buga kwanten wasa tsakanin Barcelona da Real Madrid a gasar cin kofin La Liga, inda suka ta shi 0-0 a Camp Nou.

A karawar ta hamayya da ake kira El Clasico, kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya kafa tarihin yawan buga fafatawar har sau 43.

Hakan ne ya sa ya haura wasu 'yan wasan Barca da na Real da suka buga El Clasicio sau 42 da ya hada da Sanchis da Gento da Xavi da kuma Messi.

Ramos wanda aka haifa a Sevilla ya fara buga El Clasico tun yana da shekara 15 ya kuma ci kwallo hudu, an kuma fara fafatawa da shi a wasa 29.

Cikin jerin El Clasico da Ramos ya yi har da guda bakwai a Copa del Rey da guda shida a Spanish Super Cup da karawa daya a Champions League tun fara wasan hamayyar a gasar La Liga ranar 19 ga watan Nuwambar 2005.