FIFA: Belgium ce ta daya a duniya a fagen tamaula

Belgium

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Belgium ta ci gaba da zama ta daya a duniya karo na biyu a jere a matakin wadan da ke kan gaba a fagen kwallon kafa.

Belgium wadda ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a 2020, ta lashe dukkan wasanni 10 da ta buga a shekarar nan.

Faransa mai rike da kofin duniya ta ci gaba da zama ta biyu a duniya, sai Brazil wadda take ta uku, Ingila ta hudu a duniya.

Qatar wadda za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022, ita ce kan gaba wajen taka rawar gani a 2019, bayan da ta lashe kofin nahiyar Asia.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa za ta bayyana jerin kasashen da ke kan gaba a fagen tamaula nan gaba a 20 ga watan Fabrairun 2020.

Ga jerin kasashe 10 da ke kan gaba wajen taka rawar gani a tamaula:

  • Belgium
  • France
  • Brazil
  • England
  • Uruguay
  • Croatia
  • Portugal
  • Spain
  • Argentina
  • Colombia