Arsenal za ta bayyana daukar Arteta ranar Juma'a

Arteta Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ana sa ran Arsenal za ta sanar da daukar Mikel Arteta a matsayin sabon kocinya ranar Juma'a.

Wasu rahotanni na cewar Arteta, ya yi ban kwana da Manchester City a safiyar Alhamis.

Akwai rade-radin cewar City ba ta ji dadin yadda Gunners ke jan kafa kan batun daukar kocin ba, amma ba za ta hana Arteta maye gurbin Unai Emery a Emirates ba.

Ana sa ran Arsenal za ta kammala biyan kimanin fam miliyan daya kafin a karkare cinikin mataimakin Pep Guardiola.

Gunners ta soke gana wa da 'yan jarida ranar Alhamis kan wasan Premier da Arsenal za ta yi da Everton ranar Asabar.

Ana sa ran kocin rikon kwarya Freddie Ljunberg zai ja ragamar Arsenal a Goodison Park, inda Arteta zai kalli karawar.

Arsenal ba ta fayyace tana zawarcin Arteta ba, duk da fafatawa da kungiyoyin suka yi a Premier ranar Lahadi a Emirates, inda City ta yi nasara da ci 3-0.

An dauki hoton babban jami'in Arsenal, Vinai Venkatesham a kofar gidan dan kasar Spaniyar, bayan tashi daga wasa.

Labarai masu alaka