Makomar Aubameyang, Havertz, Sane, Pogba, Guardiola da Xhaka

Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Man United da City da Liverpool na ribibin Kai Havertz

Dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, yana son barin Arsenal. (Mirror)

Bordeaux na son karbo dan wasan gaba na Chelsea Olivier Giroud a Janairu, amma dan wasan mai shekara 33 ya fi son ya koma Inter Milan. (Goal)

Tsohon wasan wasan Manchester United da Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, a shirye yake ya koma Everton da zarar kulub din ya dauki Carlo Ancelotti a matsayin koci. (Talksport)

Paris St-Germain na tattaunawa da Juventus kan musayar dan wasan Jamus Emre Can, mai shekara 25, domin karbo dan wasan Argentina Leandro Paredes, mai shekara 25. (Mail)

Manchester City da Real Madrid na hamayya game da wasan baya na PSG mai shekara Marquinhos. (Le10sport - in French)

Manchester City da Manchester United da Liverpool da Real Madrid da Barcelona na ribibin sayen matashin dan wasan Jamus mai shekara 20 Kai Havertz daga Bayern Munich. (Sun)

Manchester City ta ce ta girgiza kan yadda Arsenal ta sanar da daukar Mikel Arteta a matsayin kocinta inda sai dai ta gani a talabijin da kafofin sada zumunta na intanet. (Mail)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Dan wasan Manchester City na Jamus Leroy Sane, mai shekara 23, ya yanke shawarar komawa Bayern Munich.(Bild - in German)

Wakilin Paul Pogba Mino Raiola ya ce dan wasan tsakiyar na Faransa mai shekara, 26 yana son ci gaba da taka leda a Manchester United da kuma lashe kofuna amma yana son kara samun kwarin guiwa daga kulub din. (Telegraph)

Raiola ya bayar da hakuri kan yadda ya kasa cimma yarjejeniya tsakanin Pogba da kocin Real Madrid Zinedine Zidane. (Star)

Sannan United ta ki amincewa a alakanta Pogba da dan wasan RB Salzburg ta Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19. (Standard)

Makomar Pep Guardiola a matsayin kocin Manchester City ta dogara ne da goyon bayan da ya samu a gasar cin kofin zakarun Turai. (The Athletic, via Mirror)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer yana cike da fatan sayen 'yan wasa a Janairu. (Manchester Evening News)

United na cike da fatan samun sabbin 'yan wasa a wata mai zuwa. (Goal)

Dan wasan Arsenal dan kasar Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 27, an alakanta shi da Hertha Berlin inda ake hasashen zai koma taka leda a Bundesliga a Janairu. (ESPN)