Premier League: Arsenal ta tashi wasa babu ci

David Luiz

Asalin hoton, Getty Images

Wasa ya tashi babu ci tsakanin Arsenal da Everton a filin wasa na Goodison Park a makon Premier na 18.

Wannan ne wasa na farko da aka tashi ba tare da an zira wa Arsenal kwallo ba a cikin 15 da ta buga na baya-bayan nan a Premier.

Sai da aka yi minti 44 Arsenal ba ta kai hari na-ci ba, wanda shi ne mafi tsawo da ta taba yi a Premier tun watan Mayun 2015.

Everton ta yi yunkurin samun maki uku ganin cewa a gidanta ake yin sa, sai dai ba ta amfana da damarmakin da ta samu ba duk da cewa ba su da yawa.

Masu horarwa na rikon kwarya Duncan Ferguson da kuma Freddie Ljungerg ne suka jagoranci kungiyoyin kuma shi ne wasansu na karshe a matsayin kociyoyi a kumngiyoyin.

Tun a jiya Juma'a Arsenal ta bayar da sanarwar daukar Mikel Arteta domin maye gurnbin Unai Emery, yayain da shi kuma Carlo Ancelotti zai maye gurbin Marco Silva a Everton.

Yanzu haka Arsenal tana mataki na 9 a teburi da maki 23, yayin da Everton take mataki na 15 da maki 19.