La Liga: Messi ya ci kwallo 50 a 2019

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Messi ya shirya tsaf don zama wanda ya fi zira kwallye a raga a nahiyar Turai baki daya a 2019

Lionel Messi ya ci kwallonsa ta 50 a shekarar 2019 yayin da Barcelona ta casa Deportivo Alaves da ci 4-1.

Luis Suarez ne ya bayar da kwallo aka ci har uku rigis sannan ya ci ta hudu, abin da ya sa Barca ta dare saman teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Real Madrid a mataki na biyu.

Antoine Griezmann ne ya fara jefa kwallo a raga, Arturo Vidal ya kara ta biyu kafin daga baya Pere Pons ya ci wa Alaves.

Messi ya ci wa Barca kwallo tun daga yadi na 25 sannan sai Suarez da ya ci finareti bayan an taba kwallo da hannu.

Barcelona ta kare shekarar 2019 ba tare da an ci ta a gida ba - ta ci wasa 24, ta yi canjaras hudu - wanda shi ne mafi tsawo da ta yi tun shekarar 2011 a filin wasa na Camp Nou.

Barca ce za ta ci gaba da kasancewa a matsayi na daya har sai idan Real Madrid ta doke Athletic Bilbao da kwallo shida a gobe Lahadi.

Tun farko an hana kwallon da Messi ya ci, kafin daga bisani ya ci kwallonsa ta 50 ga Barca da Argentina a 2019.

Messi ya shirya tsaf domin zama dan wasan da ya fi zira kwallaye a raga a nahiyar Turai da kwallo 34 cikin wasan La Liga 32 da ya buga, inda ya wuce saura da kwallo biyar.

Kuma sau tara kenan yana kai wa irin wannan matsayi a cikin shekara 10 da suka gabata.