Serie A: Lukaku ya ci biyu a nasarar Inter Milan

Romelu Lukaku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Inter Milan ce ta daya a teburin Serie A

Romelu Lukaku ya ci kwallo biyu sannan ya bayar an ci daya a wasan da Inter Milan ta doke Genoa da 4-0 a wasan Serie A mako na 17.

Yanzu haka Inter Milan za ta karkare shekarar 2019 a matsayi na daya a saman teburi da maki 42 duk da cewa Juventus ma 42 din gare ta - tazarar kwallo shida ce tsakaninsu.

Tsohon dan wasan Manchester United din ya fara jefa kwallo ne a minti na 31 sannan ya bai wa Roberto Gagliardini ya ci ta biyu a minti na 33.

Lukaku ya jefa ta uku a minti na 71, sannan Sebastiano Esposito ya ci ta hudu a bugun finareti.

Inter tana saman Juventus, wadanda suka lashe gasar ta Serie A sau takwas a jere kuma a haka za su yi bikin Kirsimati abinsu.