Premier League: Man City ta gwada wa Leicester kwanji

Asalin hoton, Getty Images
Man City ta rage tazara tsakaninta da Liverpool
Manchester City ta lallasa Leicester City da ci 3-1 ta kuma rage maki uku da ke tsakaninsu yayin suke rububin zama a cikin 'yan hudun saman teburi.
Tun daga farko har karshen wasan City ce ta rike kwallon da kaso mafi yawa.
Leicester ce ta fara jefa kwallo a wasan ta kafar dan wasanta Jamie Vardy a minti na 22 da fara wasan.
Wannan ce dai kwallo ta 17 ga dan wasan da ke kan gaba a yawan kwallaye a gasar Premier, kuma yana cikin wadanda suka fi yawan cin Mancester City a gasar shi da Sadio Mane.
Bayan minti takwas da cin kwallon sai tsohon dan wasan kungiyar ta Leicester Riyad Mahrez ya farke wa City a minti na 30.
Manchester City ta ci gaba da kai hare-hare ta ko'ina, abin da yasa ta samu finareti ta kafar dan wasan gabanta Raheem Sterling.
Ilkay Gundogan ne ya buga finaretin kuma kafin hutun rabin lokaci wasa ya zama 2-1.
A minti na 69 De Bruyne ya tayar da kayar baya, ya kai wata kwallo cikin yadi na 18 inda Gabriel Jesus ya samu damar kara ta uku a ragar Leicester kuma nan take wasa ya koma 3-1.
Kwallon da ya ci ita ce ta farko da ya ci wa Manchester City a wasa 12 na gida a duka gasar da take bugawa, tun wacce ya ci a wasan Schalke 04 a watan Maris - duk 14 da ya ci wa kungiyar kafin yau ya ci ne a wasan City na waje.
Yanzu dai maki daya ne kacal ya rage tsakanin Leicester City da Manchester City a teburin Premier, inda Liverpool ta ba su tazarar maki 10.