Makomar Sancho, Gerson, Diop, Mertens da Arteta

Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arteta ya ce rashin tabbas a Man City ya sa ya karbi aikin horar da Arsenal

Chelsea za ta doke Manchester United da Liverpool a hammayar da suke kan matashin dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 19.

Chelsea a shirye ta ke ta karbo dan wasan daga Borussia Dortmund kan fam miliyan £120m. (Sun)

Mikel Arteta ya koma matsayin kocin Arsenal bayan ya kasa samun tabbaci daga Manchester City cewa zai gaci Pep Guardiola. (Mirror)

Tottenham ta tattauna da dan wasan Flamengo Gerson, mai shekara 22, kuma tana son kammala yarjejeniya da dan wasan kafin bude kasuwar musayar 'yan wasa a Janairu. (90min)

Spurs kuma tana son karbo dan wasan baya na Faransa Issa Diop, mai shekara 22, wanda West Ham ta yi wa kudi fam miliyan £50. (Sky Sports)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce a shirye yake su yi aiki da wakilin 'yan wasa Mino Raiola domin karbo dan wasan Norway mai shekara 19 Erling Braut Haaland daga RB Salzburg. (Mirror)

Chelsea ta amince ta karbo matashin dan wasa Bryan Fiabema, mai shekara 16, daga Tromso. (Metro)

Arsenal, Borussia Dortmund da Bayern Munich dukkaninsu suna sha'awar dan wasan gaba na Belgium Dries Mertens, mai shekara 32, daga Napoli kan £8.5m. (Calciomercato)

Manchester United, Everton da Southampton suna cikin manyan kungiyoyin da ke son karbo dan wasan Faransa Jean-Clair Todibo, mai shekara 19,daga Barcelona kan £17. (Sport)

AC Milan da Atletico Madrid suna son sayen dan wasan tsakiya na Manchester United na Serbia Nemanja Matic, mai shekara 31. (La Gazzetta dello Sport via Football Italia)