United ta sha kashi a hannun ta kasan teburi

De Gea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

David de Gea ne ya yi kuskuren da ya kai ga cin kwallon farko

Manchester United ta sha kashi a hannun Watford da ke karshen tebur da ci 2-0.

Wannan ce nasara ta biyu da Watford ta samu a kan Man United a gasar Premier - ta yi rashin nasara sau 11 cikin wasa 13 tsakaninta da United.

A minti 45 na farko babu wani abin a zo a gani da kungiyoyin suka taka domin kuwa ba kai hari na-ci ba ko daya.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kwallon ta sauya, inda Ismaila Sarr dan kasar Senegal ya jefa kwallo ta farko.

Dan wasan dai ya buga kwallon ne ba tare da wata cikakkiyar dama ba, amma golan United De Gea ya yi mata kamun kaza kuma ta fada raga.

David de Gea ya yi kuskuren da ya kai ga cin kwallo har sau shida tun fara kakar Premier ta bara, sama da kowanne mai tsaron raga kenan a Premier.

Minti hudu da cin kwallon farko Sarr ya samu finareti ta bangaren Wan-Bissaka bayan ya doke shi, kuma babu bata lokaci alkalin wasa ya busa bugun daga-kai sai-mai-tsaron-raga.

Asalin hoton, Getty Images

Troy Deeney ne ya ci finaretin, kuma ya ci kwallo a wasansa hudu cikin biyar da ya buga tsakaninsu da Man United a Premier a gida - dukkanninsu daga bugun finreti.

Wannan ne karon farko ma da Watford ta ci kwallo a cikin wasa hudu a Premier ta bana.

Duk da wannan nasarar da Watford ta samu har yanzu tana kasan teburi, makinta daidai da Norwich ta biyun karshe.

Ita kuma Manchester United na nan a matsayi na takwas da maki 25.