'Yan takarar gwarzon kwallon kafar Afirka na 2019

Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF ta bayyana 'yan kwallo uku da za a zabi gwarzon da babu kamarsa a 2019.

Cikin ukun da ta sanar sun hada da dan wasan tawagar Algeria da Manchester City, Riyad Mahrez da na Masar da Liverpool, Mohamed Salah da na Senegal da Liverpool, Sadio Mane.

Mane da Salah sun taimaka wa Liverpool ta lashe kofin Zakarun nahiyoyi, kuma Salah na takara karo na uku a jere.

Mahrez shi ne ya ja ragamar Aljeria ta lashe kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda Mane ya taimaka wa Senegal zuwa wasan karshe a 2019.

Haka kuma an fitar da sunayen mata uku da za a zabi wadda babu kamarta a fagen kwallon kafar Afirka a shekarar nan.

Wadan da aka bayyana sun hada da Ajara Nchout ta tawagar Kamaru da kungiyar Valerenga da Asisat Oshoala ta Najeriya Barcelona da 'yar wasan tawagar Afirka ta Kudu mai taka leda a Beijing Phoenix, Thembi Kgatlana.

Koci-Koci da daraktan tsare-tsare da kyaftin din mambobin tawagogin kwallon kafar Afirka ne za su yi zaben gwarzayen bana.

Za a bayyana wadan da suka yi fice a Afirka a wani biki da CAF za ta gudanar ranar 7 ga watan Janairu a otal mai suna Hurghada da ke Masar.

Dan kwallon da babu kamarsa a bana:

 • Mohamed Salah (Masar da Liverpool)
 • Riyad Mahrez (Algeria da Manchester City)
 • Sadio Mane (Senegal da Liverpool)

Macen da ta yi fice a tamaula a bana:

 • Ajara Nchout (Kamaru da Valerenga)
 • Asisat Oshoala (Najeriya da Barcelona)
 • Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu da Beijing Phoenix )

Dan wasan da ya yi kwazo a kungiyar Afirka a bana:

 • Anice Badri (Tunisia da Esperance)
 • Tarek Hamed (Masar da Zamalek)
 • Youcef Belaïli (Algeria da Esperance / Ahli Jeddah)

Matashin dan kwallon da babu kamarsa a Afirka a bana:

 • Achraf Hakimi (Morocco da Borussia Dortmund)
 • Samuel Chukwueze (Najeriya da Villarreal)
 • Victor Osimhen (Najeriya da Lille)

Kocin da babu kamarsa a bana:

 • Aliou Cisse (Senegal - Senegal)
 • Djamel Belmadi (Algeria - Algeria)
 • Moïne Chaâbani (Tunisia - Esperance)

Macen da ta fi yin fice a fagen koci a bana:

 • Alain Djeumfa (Kamaru)
 • Desiree Ellis (Afirka ta Kudu)
 • Thomas Dennerby (Najeriya)

Tawagar kwallon kafa ta maza da ta fi yin bajinta a bana:

 • Algeria
 • Madagascar
 • Senegal

Tawagar kwallon kafa ta mata da babu kamarta a bana:

 • Kamaru
 • Najeriya
 • Afirka ta Kudu