Dan Ali ya kashe Inda a damben Abuja

Dan Ali da Inda

Dan Alin ba ta isarka ya kashe Inda a damben gargajiya da suka fafata a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei ranar Lahadi a Abuja, Najeriya.

Tun farko a wasan damben safiyar Lahadi, makadin 'yan dambe ne ya kira Inda fili yake masa keda, sai dan Ali ya kama shi dambe.

Wasu 'yan wasa daga Arewa sun so su hana karawa tun farkor, amma Inda ya ce zai yi dambe da Dan Ali daga Arewa.

Haka suka shiga damben, Inda ya dunga kai bugu daya baya daya ya kuma samu dan Ali, amma ko gizau bai yi.

Bayan da suka ci gaba da dambe ne, sai Dan Ali ya yi nasarar buge Inda, kuma a turmin farko.

Shi kuwa Abdurrazak Ebola daga Kudu ya yi dambe da Shagon Asha ruwa Guramaga, inda suka yi turmi biyu babu kisa aka raba su.

An yi damben cin Amana tsakanin Shagon Audu Dan Crespo daga Arewa da Shagon Bahagon Dutsen Mari Guramada.

Bayan da suka taka dambe ne, sai suka ci gaba da dukan junansu da har suka kai daf da filin wasa sai alkali Roget ya hura, amma basu dai na dukun junansu ba sai kawai Bahagon Audu Dan Crespo ya yi gwiwa.

Nan da nan alkalin wasa ya hura usur, kuma Shagon Bahagon Dutsen Mari ya juya zai fita daga fili, sai kawai Bahagon Audu dan Crespo ya naushe shi, haka ya fadi wanwar da kyar ya farfado.

Wasu damben da aka yi Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Jamus da Autan Sama'ila daga Kudu babu kisa.

An kuma yi kazamin dambe tsakanin Dogon Aleka daga Kudu da Dogon Inda daga Arewa, sai dai babu kisa.

Shi kuwa Shagon Na sigari daga Kudu ya buge Shagon Bahagon Alin Tarara daga Arewa.