Fifa ta yi wa Najeriya kwalelen bakuncin kofin duniya

Under 20 World Cup

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bai wa Costa Rica da Panama izinin karbar bakuncin gasar kofin duniya ta mata 'yan shekara 20 maimakon Najeriya.

Bayan da hukumar kwallon kafar duniya ta kai ziyara kan wuraren da Najeriya za ta yi wasannin da abubun da ta tanada, aka rinka sukar ta, kan siyasa da tsaro.

Duk da sukar da aka dinga yi wa kasar, mahukuntan Najeriya sun fayyace shirin da suke yi na karbar bakuncin gasar da tanade-tanaden da suka yi don cinma nasara.

Najeriya ta tsara yin amfani da filin wasa da ke jihar Legas da Benin da Asaba da kuma Uyo tun farko.

Sai dai kuma Fifa ta amince da bai wa Costa Rica da Panama izinin karbar bakuncin gasar kofin duniya ta mata 'yan shekara 20, bayan da ta kai wa kasashen ziyarar gani da ido.

Najeriya ta taba karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta maza 'yan kasa da shekara 20 a 1999 da ta 'yan kasa da shekara 17.

Najeriya tana daga kasashe hudu da ke kai wa dukkan gasar mata ta duniya 'yan shekara 20 da ya hada da Amurka da Jamus da Brazil, tun da aka fara wasannin shekara 17 da ta wuce.

Falconets ta kai wasan karshe a 2010 da 2014 amma ta yi rashin nasara duk a hannun Jamus.