Pillars ta hada maki uku a gasar Firimiyar Najeriya

Pillars

Asalin hoton, Npfl

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasara a kan FC Ifeanyi Ubah da ci 1-0 a wasan mako na goma a gasar cin kofin Firimiya Najeriya ranar Lahadi.

Pillars wadda take da kwantan wasa daya ta ci kwallon ne ta hannun Mustapha Musa a fafatawa da suka yi a filin wasa da ke Kofar Mata a Kano,

Da wannan sakamakon Pillars wadda ta yi 1-1 a Heartland ranar Laraba, yanzu tana da maki 13 kenan.

Sauran sakamakon wasannin mao na 10 da aka fafata kuwa:

  • Nasarawa Utd 1-0 Heartland
  • Rivers Utd 2-1 Sunshine Stars
  • Plateau Utd 1-0 Wolves
  • Lobi 1-0 Katsina United
  • Kwara Utd 1-0 Rangers
  • MFM 2-0 Adamawa Utd
  • Dakkada 0-1 Akwa Utd
  • Wikki 1-1 Abia Warriors