Lazio ta ci Juventus ta lashe Italian Super Cup

Lazio

Asalin hoton, Getty Images

Lazio ta doke Juventus 3-1 ta kuma lashe Italian Super Cup a karawar da suka yi a Riyadh, Saudi Arabia.

Lazio ce ta fara cin kwallo ta hannun Luis Alberto daga baya ne Juventus ta farke ta hannun Paulo Dybala.

Daga baya ne Lazio ta kara na biyu ta hannun Senad Lulic saura minti 17 a tashi daga wasan da aka bai wa dan kwallon Juventus, Rodrigo Bentancur jan kati.

Daga karshe ne Lazio ta kara na uku ta hannun Danilo Cataldi a bugun tazara.

Wannan ne karo na biyu da aka doke Juventus a hannun Maurizio Sarri a bana, kowanne 3-1 a hannun Lazio.

Haka kuma wannan ne karo na takwas da Juventus ke buga wasan karshe a Super Cup, wanda take dauka tare da Serie A, hudu daga ciki Lazio take doke wa.