Premier League: Chelsea ta casa Tottenham har gida

Tawagar Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Willian ne ya ci kwallon biyu

Chelsea ta doke Tottenham da ci 0-2 har gida a wasan Premier mako na 18.

Dan wasan Chelsea Willian ne ya ci kwallo biyun duka, wanda hakan ya bai wa kungiyarsa damar tsira da maki uku a fafatawar.

A minti na 12 da fara wasan ya jefa kwallo ta farko cikin wani salo na kwarewa bayan ya dakko ta ta bangaren hagu kuma ya buga ta tsakanin 'yan bayan, ta fada raga.

Ana daf da juyawa hutun rabin lokaci ne Chelsea ta samu finareti, bayan wata haduwa da aka yi tsakanin golan Tottenham Gazzaniga da dan bayan Chelsea Alonso.

Ya dauki alkalin wasan kusan minti uku kafin a gama tabbatar da ko finareti ne ko akasin haka, daga karshe kuma aka gano finareti ne kuma take Willaim ya ci.

Tottenham ta dawo da karsashinta daga hutun rabin lokacin da nufin rama kwallayen da aka zira mata.

Sai dai a minti na 62 Son Heung-min ya yi ketar ramuwa ga Rüdiger, wanda hakan ya jawo aka kore shi daga wasan.

Wannan ne jan kati na uku da dan wasan ya samu a shekarar 2019, wanda rabon da a yi hakan tun 2010 da Lee Cattermole ya samu.

Yanzu dai Chelsea ta bayar da tazarar maki hudu ga Sheffield United da ke biye mata, maki shida kuma ga Tottenham da ta cinye a yau.

An samu hayaniya yayin wasan daga magoya bayan Tottenham - kalaman nuna wariyar launin fata daga magoya baya suka rika furtawa.

Hakan ya janyo an yi sanarwa har sau biyu a lasifika. Sanarwar ta ce: "Ku sani babu wata damar nuna kalaman wariyar launin fata a harkar kwallon kafa."

Wannan ce rashin nasara ta farko da Jose Mourinho ya gamu da ita a gida tun bayan karbar aikin horar da Tottenham a watan da ya gabata.