Cavani zai koma Atletico, Arsenal za ta sayi Mertens

Edinson Cavani

Asalin hoton, Getty Images

Edinson Cavani na PSG ya yarda ya koma Atletico Madrid ta kasar Sifaniya, sai dai har yanzu kungiyoyin ba su cimma yarjejeniya ba tukunna.

Sky Sports ta ruwaito cewa kwantaragin dan wasan mai shekara 32 zai kare ne a karshen kakar nan, kuma idan cinikin bai fada ba a watan Janairu to dan wasan zai koma Atletico a kyauta.

Sabon kocin Arsenal Mikel Arteta yana son daukar dan wasan gefen Napoli mai suna Dries Mertens, dan shekara 32, a watan Janairu mai kamawa yayin da kwantaragin dan kasar Belgium din ke karewa a karshen kakar bana. (Calciomercato)

Har wa yau, Arsenal din tana son daukar Kevin Volland dan kasar Jamus mai shekara 27 daga Bayer Leverkusen. (Sky Sports)

Manchester United da kuma wasu kungiyoyin Bundesliga na son daukar dan wasan Birmingham City, Jude Bellingham mai shekara 16, bayan ya fara buga wasa a babbar kungiyar kulob din. (Telegraph)

United din har wa yau ba za ta sabunta kwantaragin Nemanja Matic ba, dan wasan tsakiyarta kuma dan kasar Serbia, yayin da kwantaraginsa zai kare a watan Yunin 2020. (Express)

Everton ta yi wa sabon kocinta Carlo Ancelotti alkawarin cewa za ta ba shi kudin sayen 'yan wasa a watan Janairu, yayin da dan kasar Italiyan yake shirin fara aiki. (Star)