Bukayo Saka ya kasa zabi tsakanin Najeriya da Ingila

Bukayo Saka

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Arsenal, Bukayo Saka wanda ya cancanci ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Najeriya da ta Ingila tamaula ya ce ya rasa wadda zai zaba.

Saka wanda iyayensa 'yan Najeriya ne ya buga wa matasan Ingila kwallo, zai iya yi wa babbar tawagar wasa ko ta Super Eagles.

Sai dai matashin dan wasan Arsenal ya ce kawo yanzu babu wata tawagar da ta tuntube shi don sanin makomarsa.

Dan kwallon ya fara buga gasar Premier a Arsenal yana da shekara 17, hakan ya sa ya kafa tarihin wanda aka haifa a shekarar 2001 da ya buga gasar.

Saka ya fara buga wa Arsenal tamaula karkashin koci Unai Emery, wanda Gunners ta sallama.