An tsayar da ranar wasan Real da Atletico a La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid

Mahukuntan gasar cin kofin La Ligar Spaniya sun tsayar da ranar buga gasar cin kofin La Liga tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid.

An bayyana ranar 1 ga watan Fabrairun 2020, domin buga wasa na biyu tsakanin su a gasar cin kofin La Liga, karawar mako na 22 a Santiago Bernabeu.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar bana a wasan na hamayya ranar 28 ga watan Satumba, inda suka tashi karawar babu ci a gidan Atletico.

Bayan da aka buga wasa 18 a gasar La Liga, Real Madrid za ta buga karawar gaba ranar 4 ga watan Janairun 2020, inda za ta ziyarci Getafe.

A kuma ranar ta Asabar ce Atletico Madrid na gida, inda za ta kece raini da Levante.

Bayan da aka kammala zagayen farko a gasar La liga, Real Madrid tana ta biyu a teburi da maki 37, ita kuwa Atletico tana ta hudu da maki 32.