An cire hancin mutun-mutumin Ibrahimovich

Status

Asalin hoton, Broes syd

Wasu da ba a san ko su waye ba, sun cire hancin butun butumin Zlatan Ibrahimovic, wanda aka aje a wajen filin wasa na Malmo da ke Sweden.

Wannan ne hari na baya bayan nan da aka kai wa butun butumin, tun bayan da aka bayar da sanarwar Ibrahimovich ya sai hannun jari a kungiyar hamayya.

Wanda ya sassaka butun butumin, Peter Linde ya yi kida da mutane su dai na lalata aikin da ya yi.

Ibrahimovich tsohon dan wasan Ajax da Juventus da Inter da Barcelona da AC Milan da Paris St Germain da Manchester United ya bar LA Galaxy ta Amurka, bayan kammala gasar bana.

A ranar 27 ga watan Nuwamba aka sanar da cewar Ibrahimovich ya sayi hannun jari a kungiyar Hammarby kaso 25 cikin 100.