Ljungberg zai taimaka wa Arteta aiki a Arsenal

Fredie Lunberg

Asalin hoton, Getty Images

Freddie Ljungberg zai ci gaba da aiki a cikin masu taimaka wa kocin Arsenal kamar yadda Mikel Arteta ya sanar.

Ljungberg wanda ya buga wa Arsenal tamaula tsakanin 1998 zuwa 2007, ya karbi aikin rikon kwarya, inda ya ja ragamar wasa shida ya ci daya daga ciki, tun bayan sallamar Unai Emery.

A cikin watan Nuwamba aka kori Emery, wanda ya yi aiki da Ljungberg a matakin mataimakin sa.

Arteta tsohon mataimakin Pep Guardiola, zai ja ragamar Arsenal a karon farko ranar 26 ga watan Disamba a karawa da Bournemouth.

Arteta tsohon dan kwallon Arsenal, ya koma Gunners shekara hudu bayan da Ljungberg ya bar Emirates.

Arteta bai bayyana sunayen wadan da za su taimaka masa gudanar da aikin ba, amma tsohon dan wasan Everton da Manchester United, Steve Round yana cikin su.