Chelsea na da damar karbo Isco, Real ta hakura da Pogba

Isco

Asalin hoton, Getty Images

RB Leipzig ta ce za ta yi hamayya da Manchester United domin karbo dan wasan Norway Erling Haaland daga Salzburg. (Mail)

An ba Chelsea damar karbo Isco, mai shekara 27, kan fam miliyan £44 yayin da Real Madrid, ke son amfani da kudin domin karbo dan wasan tsakiya na Tottenham mai shekara 27 Christian Eriksen. (Mirror)

Napoli da Roma na farautar dan wasan Arsenal dan kasar Bosnia-Herzegovina Sead Kolasinac, mai shekara 26. (Sky Sports)

Real Madrid ta shaida wa wakilin Paul Pogba, Mino Raiola cewa ba ta bukatar dan wasan mai shekara 26 a Janairu. (Mail)

Tottenham sai ta biya fam miliyan £50 kafin ta karbo dan wasan baya na Faransa Issa Diop, mai shekara 22, daga West Ham. (Express)

Spurs kuma tana son karbo dan wasan tsakiya na Lille Boubakary Soumare, mai shekara 20 wanda Manchester United ta ke nema. (L'Equipe - via Football 365)

Atletico ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Paris Saint Germain kan dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 32. (Star)

Manchester United ta ba Ole Gunnar Solskjaer goyon bayan karbo dan wasan gaba na Juventus dan kasar Croatian Mario Mandzukic, mai shekara 33. (Express)