Madrid za ta shiga shekarar 2020 a bayan Barcelona

Gareth Bale

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid za ta shiga shekara ta 2020 a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona wadda take ta daya a teburin La Ligar bana.

A ranar Lahadi Real ta wi wasan mako na 18 da Athletic Bilbao a gasar La Liga, inda suka tashi karawar 0-0.

Karo na uku kenan da kungiyar da Zinedine Zidane ke jan ragama ta yi canjaras a jere, kuma wasa biyu a jere da ba ta zura kwallo a raga ba.

Haka kuma Real din kwallo 14 ta zura a raga, bayan kammala zagayen farko a wasannin bana.

Karim Benzema ya ci kwallo 12 a wasa 17 da ya yi wa Madrid, Lionel Messi ne ke kan gaba da 13 a raga a wasannin.

Idan ka hada da kwallon da Messi ya ci 13 da na Luis Suarez 10 da na Antoine Griezman bakwai sun zama 30, wadda Real guda 33 gabaki daya ta ci a kakar bana.

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos shi ne na biyu a yawan cin kwallo a kungiyar da guda uku sai masu bibiyu da suka hada da Toni Kroos, Luka Modric, Gareth Bale, Rodrygo Goes and Fede Valverde.

Real ta barar da maki uku a Santiago Bernabeu a wasan bana, a karawar da ta yi da Real Valladolid da Betis da kuma Athletic.