Zidane ya ja ragamar Real Madrid wasa 184

Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Zinedine Zidane ya ja ragamar Real Madrid wasa 184, bayan da suka tashi 0-0 da Athletic Bilbao ranar Lahadi a gasar La Liga.

Hakan ne ya sa ya zama na hudu a jerin wadan da suka horas da Real wasanni da yawa, ya kuma haura tarihin Molowny wanda ya yi 183.

Kawo yanzu wadan da ke gabansa sun hada da Beenhakker wanda ya ja ragamar wasa 197, sai Del Bosque da ya horas sau 246 da kuma Miguel Munoz mai 605.

Jerin wasannin da Zidane ya ja ragama sun hada da LaLiga sau 125 da gasar Champions League 39 da karawar Copa del Rey 12 da fafatawar Club World Cup 4 da gumurzun European Super Cup 2 da kuma wasan Spanish Super Cup 2.

Cikin wasa 184 da Zidane ya ja ragamar Real ya lashe kofi tara da suka hada da Champions Legaue 3 da Club World Cups 2 da European Super Cup 2 da La Liga 1 da kuma Spanish Super Cup 1.