Chamberlain ba zai buga wa Liverpool wasanni ba

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Alex Oxlade-Chamberlain ba zai buga wa Liverpool wasa biyu ba, sakamakon jinya da zai yi.

Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 26, sai sauya shi aka yi a raunin da ya yi a lokacin wasan cin kofin duniya na Zakarun nahiyoyi.

A karawar ce Liverpool ta lashe kofin, bayan da ta doke Flamengo ta Brazil da ci 1-0 ranar Asabar a Qatar.

Alex Oxlade-Chamberlain bai buga wa Liverpool kusan fafatawar kakar 2018-19 ba, sakamakon jinya da ya yi.

Klopp ya ce babu yadda Chamberlain zai buga wa Liverpool wasan Premier da za ta yi a Leicester City ranar Alhamis a King Power.

Da kuma wanda za ta karbi bakuncin Wolverhampton a Anfield ranar Lahadi, kuma karawa ta tara da za ta yi a watan Disamba.

Haka kuma Klopp ya bayyana wasu 'yan wasan Liverpool da ke yin jinya da suka hada da Fabinho da Dejan Lovren da kuma Joel Matip.

Kofin Zakarun nahiyoyin duniya shi ne na biyu da Liverpool ta lashe a bana, bayan Uefa Super Cup da ta dauka, inda ta yi nasara a kan Chelsea a bugun fenariti.

Haka kuma Liverpool ita ce ta daya a teburin Premier da maki 49 da kwantan wasa daya da West Ham United.