Wasa tara Liverpool za ta yi cikin watan Disamba

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Asabar Liverpool ta lashe kofin Zakarun nahiyoyin duniya, bayan da ta doke Flamengo da ci 1-0 a Qatar.

Nasarar lashe kofin da Liverpool ta yi shi ne na biyu, bayan da ta dauki Uefa Super Cup a bana, inda ta doke Chelsea a bugun fenariti.

Kawo yanzu Liverpool wadda za ta buga wasanni tara a cikin watan Disamba, ta buga guda bakwai.

A ranar Alhamis Liverpool za ta ziyarci Leicester City a wasan Premier karawar mako na 19.

Sai a ranar Lahadi ne za ta yi wasanta na tara a watan na 12 shekarar 2019 da Wolverhampton a Anfield karawar Premier.

Liverpool wadda ke jan ragamar teburin Premier da kwantan wasa da Westy Ham United ta ci kwallo 15 aka zura mata uku a raga.

Ga jerin wasannin Liverpool tara a watan Disamba:

4 ga watan Disamba Premier League

  • Liverpool 5 - 2 Everton

7 ga watan Disamba Premier League

  • Bournemouth 0 - 3 Liverpool

10 ga watan Disamba Champions League

  • RB Salzburg 0 - 2 Liverpool

14 ga watan Disamba Premier League

  • Liverpool 2 - 0 Watford

17 ga watan Disamba Carbao Cup

  • Aston Villa 5 - 0 Liverpool

18 ga watan Disamba Fifa World Cup Cup

  • Monterrey 1 - 2 Liverpool

21 Disamba Fifa World Cup Cup

  • Liverpool 1 - 0 Flamengo

Wasannin da Liverpool za ta yi:

26 Disamba Premier League

  • Leicesterda Liverpool

29 Disamba Premier League

  • Liverpool da Wolves