'Yan Eritiriya sun yi batan dabo bayan buga gasa a Uganda

Eritrea

Asalin hoton, Getty Images

'Yan wasan Eritiriya bakwai sun gudu daga sansaninsu, bayan kammala gasar kwallon kafa ta Kudancin Afirka da aka yi a Uganda.

Sauran 'yan kwallon sun koma gida, bayan kammala gasar da ake kira CECAFA, wadda suka yi na biyu a wasanni.

Wannan ne karo na biyu da 'yan kwallon Eritrea ke gudu daga sansaninsu, bayan da 'yan wasa biyar suka arce a baya.

Mahukuntan wasannin suna ta neman 'yan kwallon da suka tsere, an kuma sanar da jami'an tsaro lamarin.

A shekarar 2015 'yan kwallo 10 ne suka ki komawa gida, bayan da suka buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a Botswana.

Shekara biyu tsakani aka amincewa 'yan wasa 15 har da likitansu mafaka a Uganda, bayan zuwa gasar cin kofin kalubale.

A shekarar 2009 a gasar ta Kudancin Afirka, bayan kammala ta ne gabaki dayan 'yan kwallo suka ki komawa Eritiriya, in banda koci da jami'an tawagar.

Hukumar kare 'yancin dan Adam ta duniya, Amnesty International ta ce mutane da dama na tserewa daga kasar, inda gwamnati ke hana hakan.

Gwamnati Eritiriya ta yi watsi da zargin da ake na yawan mutanen da suke gudu daga kasar, inda ta ce lissafin bai kai wanda ake fada ba.