United za ta sayi Maddison, Pogba na son barin United

James Maddison

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tsakiyar Manchester United, Paul Pogba mai shekara 26, yana son ya bar United domin komawa tsohon kulob dinsa na Juventus. (Calciomercato)

Man United din za ta mika tayin fan miliyan 80 kan dan wasan tsakiyar Leicester City mai shekara 23, James Maddison, a karshen kakar wasa ta bana. (Daily Star)

Har wa yau, Man United za ta bai wa Erling Haaland, matashin dan wasan Red Bull Salzburg mai shekara 19, albashin fan dubu 200 a duk mako domin ya koma Old Trafford da take-leda.

Barcelona za ta sake yunkurawa domin daukar dan wasan Paris St-Germain, Neymar mai shekara 27, a karshen kakar bana. (Goal)

Chelsea tana kokarin sayen dan wasan gaban RB Leipzig kuma dan kasar Jamus, Timo Werner mai shekara 23. (Express)

Dan wasan gaban Juventus Mario Mandzukic ya kawo karshen rade-radin cewa zai koma Man United bayan ya kammala komawarsa kasar Qatar, inda zai taka wa Al-Duhai leda.

Ana sa ran Arsenal za ta sayar da daya daga cikin 'yan wasan gabanta domin sayo dan wasan gaban kungiyar Lyon, Moussa Dembele mai shekara 23. (Le10Sport - in French)

Saura kiris Edinson Cavani mai shekara 32 ya koma kungiyar Atletico Madrid daga PSG a watan Janairu. (Marca)

Kungiyoyin AC Milan da Monaco sun bi sahun Man United a yunkurinsu na daukar dan wasan bayan Barcelona kuma dan kasar Faransa, Jean-Clair Todibo mai shekara 19 a karshen kakar bana. (Calciomercato)

Kocin West Ham da ke shan matsin lamba Manuel Pellegrini, yana bukatar sayen 'yan wasa hudu a watan Janairu, sannan kuma zai iya kyale dan wasan baya Issa Diop ya bar kungiyar. (Express)