Premier League: Tottenham ta koma ta 5 a teburi

Harry kane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallo ta 10 kenan da Kane ya ci a kakar bana

Tottenham ta ci gaba da yunkurinta na shiga rukunin 'yan hudun farko a saman teburin Premier yayin da ta farke kwallon da Brighton ta zira mata sannan kuma ta doke ta.

Nasarar ta mayar da Tottenham matsayi na biyar a teburin da maki uku tsakaninta da Chelsea da ke mataki na hudu, wadda take wasa wasa da Southampton yanzu haka.

Sheffield United ka iya kamo kafar kungiyar ta Mourinho idan ta ci wasanta da Watford.

Adam Webster ne ya fara zira kwallo a raga a minti na 37, bayan an soke kwallon da Harry Kane ya ci.

Tun a minti na 24 Kane ya saka kwallo a zare amma na'urar VAR ta ce ya yi satar gida, amma bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya farke ta a minti na 53.

Kane ya zira kwallo 10 kenan a kakar bana cikin wasa 18 da ya buga.

Dele Alli ne ya kara ta biyun wadda da ita ce Tottenham ta samu makinta uku - kwallonsa ta shida kenan a kakar bana.