Ibrahimovic na tattaunawa da AC Milan

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kungiyoyi da dama suna neman Ibrahimovic mai shekara 38

Tsohon dan wasan gaban kasar Sweden da Manchester United Zlatan Ibrahimovic ya koma AC Milan ta Serie A bisa yarjejeniyar wata shida tare da zabin karin shekara.

Dan wasan mai shekara 38 ba shi da kulob bayan ya bar kungiyar LA Galaxy ta kasar Amurka a karshen kakar wasa ta gasar Major League Soccer ta bana.

Kungiyar AC Milan ta ce Ibrahimovic "zai isa birnin Milan domin gwada lafiyarsa" sannan ya hade da abokan wasansa.

"Zan koma kulob din da nake girmaamawa da kuma garin Milan da nake kauna," Ibrahimovic ya fada.

Ya buga wa AC Milan wasanni na shekara biyu daga 2010 zuwa 2012 - ya ci kwallo 42 a wasa 61 na Serie A.

Ya koma LA Galaxy ta kasar Amurka a watan Maris na 2018, inda ya ci kwallo 53 sannan kuma ya shiga cikin tawagar gasar MLS ta shekarun 2018 da 2019.

AC Milan ba ta kara daukar wani kofin kirki ba tun daga shekarar 2011 da ta dauki Serie A a karo na 18.

Tsofaffin zakarun Turai har sau bakwai, Milan suna fama a kakar bana yayin da suke matsayi na 11 a teburin Serie A da maki 21 a wasa 17.

Kungiyar ta kori kocinta Marco Giampaolo a watan Oktoba amma har yanzu ba ta sauya zani ba a karkashin Stefano Pioli.

Sun sha kashi a wasnsu na makon da ya gabata da ci 5-0 a hannun Atalanta, wanda rabon da hakan ta faru tun shekara 21.