Premier League: Chelsea ta sha kashi a Stamford Bridge

Tammy Abraham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rabon da Chelsea ta sha kashi sau biyu a jere a gida tun a 2011

Chelsea ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere a gidanta a karon farko tun shekarar 2011 bayan Southampton ta caskara ta da ci 0-2 har gida.

Masu masaukin bakin ba su yi wani kokari ba a minti 45 na farko kuma Michael Obafemi bai yi wata-wata ba ya cinye su tun a minti na 31.

Shigowar dan wasan gaba Mason Mount ta so ta kara wa tawagar Lampard azama amma ba don Fikayo Tomori ba da an kara masu ta biyu.

Kazalika, ana minti na 73 ne kuma aikin hadin gwiwa tsakanin 'yan wasan Southampton ya hango Nathan Redmond kuma ba wani bata lokaci ya cilla ta raga daga yadi na 10.

Rashin nasara ta biyar kenan da Chelsea ta yi a cikin wasa bakwai na baya-bayan nan da ta buga a Premier.

Har yanzu tana nan a mataki na hudu amma fa da maki uku tsakaninta da Tottenham da kuma Sheffield United a mataki na biyar da na shida.