Premier League: Har yanzu Arsenal na ruwa

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arteta bai fara da nasara ba a matsayin kociya

Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallonsa ta 12 a Premier ta bana yayin da Arsenal ta yunkura ta yi canjaras da Bournemouth a wasan mai horarwa Mikel Arteta na farko a kungiyar.

Dan wasan tsakiya Dan Gosling ne ya fara jefa kwallo a ragar Gunners a wani harin kusa da ya kai, kafin kyaftin din Arsenal din ya kawo mata dauki.

Aubameyang ya fara kai hari ne a bakin yadi na 18 din Bournemouth bayan kwallon ta fada kafarsa daga wani harin da Reiss Nelson ya kai.

Wasa daya kacal Arsenal ta ci cikin wasa 11 da ta buga a baya-bayan nan a Premier kuma duk da maki daya da suka samu, aiki na nan jibge ga kociya Arteta.

Aikin da ke gaban Arteta

Arsenal ta fi kusa da kasan teburi sama da samansa sannan kuma maki 24 ta zubar a cikin wasa 11 na Premier da ta buga.

Ranar Lahadi kuma za ta karbi bakuncin Chelsea sannan ta sake tarbar Manchester United ranar Laraba.

Yayin da 'yan wasan Arsenal din ke kokarin gaisawa da magoya bayansu bayan tashi daga wasan, sai ga shi ana taba wa kociya Mikel Arteta.